29 Afirilu 2016 - 17:31
Mutane 53 ne suka rasu a Aleppo dake Syria

Majalisar Dimkin Duniya da kasar Amurka sun yi Allah wadai da harin da aka kai asibitin Aleppo na kasar Syria, inda Amurka ta bukaci Russia ta ja kunne shugaba Bashar al Assad.

Sakataren Janar na Majalisar Dimkin Duniya Ban Ki Moon ya bayyana harin a matsayin abin takaici, yayin da Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya ce da gangan gwamnatin B ashar al Assad ke kai hari kan fararen hula.

Akalla mutane 53 aka kashe a tahsin hankalin da aka samu jiya a birnin Aleppo.288